Labarai
’Yan bindiga 9 sun mutu a wani artabu da Sojoji a Shanono

An kashe ’yan bindiga tara yayin artabu mai tsanani tsakaninsu da dakarun sojin kasarnan a Bakaji da Unguwar Garma, yankin Goron Dutse na Ƙaramar Hukumar Shanono, Jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar sun kai hari ne da rana tsaka, amma sojoji sun yi gumurzu da su na tsawon sa’o’i, inda suka yi nasarar fatattakar su. A artabun, an kashe ɗan sa-kai guda, yayin da wani ya jikkata.
Shugaban Kwamitin Tsaron Al’umma na Shanono/Bagwai, Alhaji Yahya Bagobiri, ya ce duk da nasarar da aka samu, ’yan bindigar sun tsere da shanu 40 tare da sace mutane shida kamar yadda paradigm news ta rawaito



