Labarai
Gwamnan Zamfara ya naɗa AIG mai ritaya a matsayin Babban Kwamandan Tsaron Jihar

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya naɗa tsohon Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, AIG Muhammad Shehu Dalijan mai ritaya, a matsayin Babban Kwamandan Rundunar Tsaron Jihar.
Sanarwar da Suleman Ahmad Tudu ya fitar ta ce naɗin ya fara aiki nan take, tare da umarnin sake fasalin rundunar domin ƙarfafa tsaro da inganta ayyuka a faɗin jihar.
Muhammad Shehu Dalijan ya taɓa rike muƙamin Kwamishinan ’Yan Sandan Zamfara daga 2023 zuwa 2025, kafin daga bisani a daga shi zuwa AIG, sannan ya yi ritaya a Yuni 2025.



