Labarai
Sojojin Amurka Sun Kai Hari Kan ’Yan ISIS a Sokoto

Sojojin Amurka sun tabbatar da kai hare-haren sama kan mayakan ƙungiyar ISIS a Jihar Sokoto a daren Alhamis, bayan buƙatar taimako daga gwamnatin Najeriya.
A cewar Ma’aikatar Tsaro ta Amurka, an gudanar da harin ne tare da haɗin gwiwar hukumomin Najeriya, inda aka kashe ’yan ta’addan ISIS da dama.
Sanarwar ta fito ne daga rundunar sojojin Amurka da ke kula da yankin Afirka, wadda ta ce harin ya kasance bisa yarjejeniyar tsaro da Najeriya.
Sai dai mazauna ƙauyen Jabo da ke Ƙaramar Hukumar Tambuwal sun ce duk da jin harin a kusa da yankinsu, zuwa yanzu babu rahoton mutuwa ko jikkata fararen hula.
Harin ya zo ne a lokacin da ake ƙara fuskantar matsalar tsaro da hare-haren ta’addanci a Arewa maso Yammacin Najeriya.




