Rundunar ’yan sandan Jihar Ogun ta sanar da kama mutane takwas da ake zargi da rajin ganin yankin Yarabawa ya balle daga Najeriya

An kama wadanda ake zargin ne a ranar Alhamis a mahadar Temidire da kuma karkashin gadar Sango-Ota, yayin da suke gudanar da zanga-zanga a karkashin wata kungiya mai suna Democratic Republic of the Yoruba.
A cewar kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Oluseyi Babaseyi, mambobin kungiyar sun tare hanyoyi ba bisa ka’ida ba, sun kunna wuta a kan tituna, sun hana zirga-zirgar ababen hawa, sannan suka kai wa jami’an tsaro hari.
Ya ce jami’an ’yan sanda sun gaggauta isa wurin, inda suka tarwatsa zanga-zangar tare da kama mutane takwas.
Kayayyakin da aka kwato sun hada da mota kirar Toyota Dyna, lasifika, tutoci, riguna da sauran kayan rajin ballewa.
Babaseyi ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
Rundunar ta kuma jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tana mai gargadin cewa ba za ta lamunci duk wani abu da zai dagula zaman lafiya ba, tare da bukatar jama’a su rika bin doka da oda da kai rahoton duk wani motsi da ake zargi ga lambobin gaggawa na rundunar.


