PDP Ta Soki Gwamnatin Tarayya Kan Jinkirin Bayyana Harin Amurka a Najeriya

Jam’iyyar adawa ta PDP ta soki Gwamnatin Tarayya kan gazawarta wajen sanar da ‘yan Najeriya game da harin saman da Amurka ta kai kan ‘yan ta’adda a Arewa maso Yammacin ƙasar nan, kafin shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da lamarin a kafafen sada zumunta.
Harin, wanda aka kai a ranar Alhamis, ya faru ne makonni bayan Trump ya ayyana Najeriya a matsayin ƙasa mai tayar da hankalin addini, wato Country of Particular Concern (CPC).
Shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa dakarun Amurka sun kai hari a Arewa maso Yammacin Najeriya, inda suka kashe ‘yan ta’adda da dama.
Daga bisani ne Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da harin, tana mai cewa an aiwatar da shi ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaron Najeriya.
Sai dai kakakin jam’iyyar PDP, Ini Ememobong, ya ce ya dace gwamnatin tarayya ta fara sanar da jama’a kafin bayanan su fito daga Amurka.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ysu Juma’a, Ememobong ya bayyana cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta yi wa ‘yan ƙasa cikakken bayani tun farko domin wayar da kan jama’a, maimakon jira ta tabbatar da wani labari da tuni ya bazu a bainar jama’a.
Ya ce, “Ya dace Gwamnatin Tarayya ta fara fitar da bayani domin sanar da ‘yan Najeriya yadda ya kamata, maimakon ta jira ta tabbatar da labarin da ya riga ya yadu, sai dai idan lamarin ya zo musu a bazata kamar sauran ‘yan ƙasa.”
Jam’iyyar PDP ta jaddada bukatar gwamnati ta inganta hanyoyin sadarwa da ‘yan ƙasa, musamman a batutuwan tsaro da ke da muhimmanci ga rayuka da zaman lafiyar al’umma.
