Ketare

Nijar Ta Hana ‘Yan Amurka Shiga Ƙasar, Ta

Jamhuriyyar Nijar ta dauki wani sabon mataki na diflomasiyya ta hanyar haramta bai wa ‘yan kasar Amurka visa, tare da hana su shiga ƙasar baki ɗaya, a matsayin martani ga matakin da Amurka ta dauka na sanya Nijar cikin jerin kasashen da ‘yan kasarsu ba za su sake samun visa ta Amurka ba.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa, wata majiyar diflomasiyya ta tabbatar da cewa bisa sabbin dokokin gwamnatin Nijar, ba za a sake bai wa duk wani ɗan Amurka visa ta kowacce hanya ba.

 

Majiyar ta ce haramcin ya shafi dukkan nau’o’in ziyara, kama daga yawon bude ido, kasuwanci, zuwa harkokin diflomasiyya, lamarin da ke nuni da mataki na dindindin na hana ‘yan Amurka sanya kafa a cikin Nijar.

 

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tsamin dangantaka tsakanin Nijar da wasu ƙasashen yammacin duniya, musamman Amurka, tun bayan sauyin mulki da ya faru a kasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button