Labarai

Gwamnatin tarayya ta ki amincewa da sabuwar bukatar belin mai shiga tsakanin yan ta’ada wato Tukur Mamu ke nema na a sake shi daga hannun hukumar tsaro ta DSS bisa dalilan lafiya

Mamu wanda ake zargi da shiga tsakani a shari’ar garkuwa da yan cikin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, a cikin takardar neman belin da tawagar lauyoyin sa karkashin jagorancin Mista Johnson Usman, ya bukaci kotun ta ba da umarnin a sake shi domin samun damar samun kulawar da ta dace.

Mamu na fuskantar tuhume tuhuman ta’addanci guda 10.

An kama shi ne a ranar 6 ga watan Satumba, 2022, a birnin Alkahira na kasar Masar, a kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya don gudanar da umrah.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button