Ƴan Sanda Sun Tabbatar da Mutuwar Mutane 6 a Sabon Harin Ƴan Bindiga a Neja

Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane shida a sakamakon wani sabon hari da ƴan bindiga suka kai kusa da ƙauyen Wawa da ke Jihar Neja.
A cewar rundunar, ƴan bindigar sun yi wa wani uba da ɗansa kwanton ɓauna yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa ziyartar ma’aikatan gona a ƙauyen Damala.
An bayyana cewa ɗan ya samu nasarar tserewa daga harin inda ya nemi agaji.
Sai dai, ƴan uwa da kuma wasu ‘yan sa-kai da suka je neman mahaifin yaron bayan harin, su ma sun faɗa hannun ƴan bindigar, inda aka sake kai musu hari.
Daga bisani jami’an tsaro sun gano gawarwaki guda shida a yankin.
Rahotanni sun ce mutumin da aka fara kai wa hari da kuma wani mutum ɗaya sun ɓace ba tare da an san inda suke ba.
An kai gawarwakin da kuma waɗanda abin ya shafa zuwa babban asibitin garin Wawa, yayin da jami’an tsaro suka ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.




