Siyasa

Tsoffin Kwamishinonin Ganduje Sun Karyata Labarin Cewa Sun Yarda da Barau Jibrin a 2027

Gamayyar tsoffin kwamishinonin da suka yi aiki a zamanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta karyata labarin da ke yawo cewa sun amince da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, a matsayin ɗan takarar gwamna a Kano a 2027.

Tsohon Kwamishinan Harkokin Musamman kuma ɗan takarar shugabancin APC na jiha, Dr. Mukhtar Ishaq Yakasai, wanda ya yi magana da yawun gamayyar, ya bayyana cewa labarin karya ne marar tushe. Ya ce sun je taron gaisuwa ne da Sanata Barau bisa gayyata, inda suka tattauna kan hadin kai da cigaban jam’iyya, ba batun marawa kowa baya ba.

Ya jaddada cewa ba a taɓa tattauna batun neman takara ko marawa Barau baya ba. Ya kara da cewa APC na da shugabanci da tsarin da ake bi wajen zaben ɗan takara, kuma za su bi shawarar jam’iyya gaba ɗaya.

Dangane da jita-jitar cewa shi kansa ya yi wani irin goyon baya, Yakasai ya ce hakan ba zai yiwu ba tunda akwai masu neman takara da dama a jam’iyyar, ciki har da A.A. Zaura, Murtala Sule Garo, da tsohon mataimakin gwamna Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.

Ya shawarci jama’a da ’yan jam’iyyar su yi watsi da labarin karya, tare da mayar da hankali ga haɗin kai da ƙarfafa APC a jihar Kano. Gamayyar ta ce za ta mara baya ga duk wanda jam’iyya ta zaɓa a 2027.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button