Labarai

CP Bakori Ya Ziyarci Shanono da Tsanyawa Don Duba Matakan Tsaro a Iyakokin Kano da Katsina

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya kai ziyarar aiki zuwa ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa domin duba yadda jami’an tsaro suka bazu a yankunan da ke kan iyakar Kano da Katsina, sakamakon ƙaruwa matsalolin tsaro kamar sace mutane da satar shanu.

A yayin ziyarar, CP Bakori ya yaba wa Rundunar Hadin Gwiwa (JTF) bisa jajircewarsu wajen kare al’umma, tare da jan hankalin jami’an da su ƙara kaimi kuma su kasance cikin shiri a ko da yaushe domin dakile barazanar ’yan bindiga.

 

Ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar ’yan sanda na aiki ba dare ba rana domin tabbatar da zaman lafiya, yana mai kira ga al’umma su rika ba da rahoto kan duk wani abin da suke zargi.

 

CP Bakori ya gode wa Gwamnatin Kano, shugabannin ƙananan hukumomi da al’umma kan haɗin kai da goyon bayan da suke baiwa jami’an tsaro, yana mai cewa hakan na taka rawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali.

Rundunar ’Yan Sandan Kano ta ce za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyi tare da shawo kan duk wani sabon kalubalen tsaro.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button