Babbar Kotun Kano Ta Daga Shari’ar Kisan Surajo Aminu Zuwa 1 ga Disamba, 2025

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 9 da ke Bompai, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hadiza Sulaiman, ta dage shari’ar kisan da ake tuhumar wasu matasa biyu da aikatawa zuwa ranar 1 ga Disamba, 2025, domin karɓar bayanan ƙarshe daga bangarorin da abin ya shafa.
Masu kara, wato Gwamnatin Kano, na tuhumar matasan Nafiu Garba Yaroro da Abdulmalik Garba da kashe matashi Surajo Aminu tun a shekarar 2019.
Ana zargin cewa rikicin ya samo asali ne bayan Surajo ya fara soyayya da wata budurwa mai suna Bahijja ’yar unguwar Dakata, wacce a baya take soyayya da Nafiu. Wannan ne ya haifar da fushi da ake zargin ya sa matasan suka caka wa Surajo wuƙa, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.
A zaman kotun na baya-bayan nan, waɗanda ake tuhuma sun kammala gabatar da shaidunsu kan zargin haɗa kai da aikata kisan kai.
Kotun ta daga zaman zuwa ranar 1 ga Disamba, 2025 domin ci gaba da shari’a tare da sauraron bayanan ƙarshe daga dukkan bangarorin.




