Shugaban PDP ya aikata cin amanar ƙasa — In ji Bayo Onanuga

Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya zargi sabon shugaban jam’iyyar PDP, Kabiru Turaki, da aikata cin amanar ƙasa bayan roƙonsa ga kasashen waje su shiga rikicin siyasar cikin gida.
Rikicin ya ɓarke ne a hedikwatar PDP da ke Abuja a ranar Talata, inda bangarori biyu na jam’iyyar suka yi hargitsi. Daga bisani, Turaki ya kira taron manema labarai, inda ya roƙi Shugaban Amurka Donald Trump da sauran ƙasashen duniya su “ceto dimokuraɗiyyar Najeriya” saboda rikicin da PDP ke fama da shi.
Turaki ya yi gargadin cewa rikicin jam’iyyar ya kai wani matsayi da ka iya zama barazana ga tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar, don haka akwai bukatar waje su kawo ɗauki.
Sai dai Onanuga ya ce wannan kira na Turaki ya yi kama da kiran shigar da ƙasashen waje cikin harkokin cikin gida, abin da ya kira “cin amanar ƙasa”.
Wannan al’amari ya faru ne kwanaki kaɗan bayan wata barazanar soja da Trump ya yi wa Najeriya, inda ya ce za a ɗauki mataki idan gwamnatin tarayya ta kasa kawo karshen kisan Kiristoci a ƙasar — kalamai da suka jawo cece-kuce a fagen siyasa.




