Labarai

Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutum 7, Ya Jikkata 11 a Jigawa

Akalla mutum bakwai sun rasa rayukansu, ciki har da direban mota, yayin da wasu 11 suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Jihar Jigawa.

 

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Shiisu Lawan Adam, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar daga Dutse, babban birnin jihar.

 

Hatsarin ya faru ne da misalin 4:30 na yamma a kauyen Jigawan Kurma, da ke kan titin Kiyawa–Azare a hanyar zuwa Bauchi.

 

A cewar SP Shiisu, motar kirar Hummer mai zuwa daga Kano zuwa Potiskum, na ɗauke da fasinjoji 18, inda tayoyi biyu suka fashe sakamakon gudu fiye da ƙa’ida da ake zargin direban ke yi. Lamarin ya haifar da hatsarin da ya yi sanadiyar mutuwar fasinjoji bakwai.

 

Mutum 11 da suka samu raunuka an garzaya da su zuwa Babban Asibitin Dutse inda aka sallami fasinjoji huɗu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button