Gwamnatin Tarayya Ta Ƙara Ƙaimi Kan Yaƙi da Ta’addanci — Ministan Yaɗa Labarai

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta tura ƙarin jami’an tsaro a sassa daban-daban na ƙasar domin murƙushe ayyukan ta’addanci, bayan wasu hare-hare da suka faru a kwanakin nan a jihohi daban-daban.
Da yake jawabi a taron manema labarai da aka gudanar a Radio House, Abuja, a ranar Laraba 19 ga Nuwamba, 2025, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗaga matakin tsaro zuwa mafi girma domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa.
Idris ya mika sakon ta’aziyyar shugaban ƙasa ga iyalan mutanen da abin ya shafa, yana mai bayyana kashe babban hafsan soji, sace dalibai a Jihar Kebbi, da harin cocin Eruku a Kwara a matsayin manyan al’amuran da ke nuna girman barazanar tsaro a ƙasar.
Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya dage tafiyarsa zuwa taron G20 a Afirka ta Kudu da wasu tarukan ƙasashen waje, domin mayar da hankali kan magance matsalolin tsaro a gida. Haka kuma ya umarci rundunonin tsaro su ƙara yawan jami’ai a Eruku da yankunan da ke kusa da ƙaramar hukumar Ekiti ta Jihar Kwara.
Ya bayyana cewa jami’an tsaro sun samu umarni na musamman domin ceto daliban Kebbi, tare da rusa hanyoyin sadarwar ‘yan ta’adda a faɗin ƙasa.
A cewar Idris, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima na can Birnin Kebbi domin ganawa da Gwamnan jihar, shugabannin tsaro da sarakunan gargajiya, da kuma iyalan daliban da aka sace.
Ministan ya yi watsi da duk wani yunƙurin da wasu ke yi na bai wa matsalolin tsaro fassarar addini, yana mai cewa laifukan sun shafi musulmi da Kirista da kabilu daban-daban. Ya ce: “Haɗin kan ƙasa shi ne makamarmu ta ƙarfi. Abokan gaba su ne ‘yan ta’adda, ba ’yan ƙasa ba.”
Ya ƙara tabbatar da cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro domin ganin an dawo da zaman lafiya da kubutar da duk masu ruwa da tsaki a tashin hankalin da aka samu.




