Gwamna Yusuf Ya Dauki Sabbin Ma’aikata 2,000 Don Ƙarfafa Fannin Ilimi

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da cewa dokar ta-baci da aka ayyana a fannin ilimi na samar da sakamako, bayan ya raba takardun ɗaukar aiki na dindindin ga sabbin ma’aikata 2,000.
Sabbin ma’aikatan sun haɗa da malaman lissafi 400 da kuma ma’aikatan tsaro (watchmen) 1,600 da aka tura zuwa makarantun sakandare a faɗin jihar.
A cewar mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, wannan mataki na daga cikin manyan nasarorin gyaran ilimi da gwamnatin Yusuf ke aiwatarwa.
A yayin taron da aka gudanar a Coronation Hall, Gwamna Yusuf ya ce wannan ɗaukar aiki mataki ne na gina ingantaccen tsarin ilimi, domin babu wata al’umma da za ta ci gaba fiye da tsarin iliminta.
Ya bayyana cewa ɗaukar malaman lissafi 400 na da nufin magance ƙarancin malamai a muhimmin fannin da ke da alaƙa da kimiyya da fasaha.
Haka kuma tura watchmen 1,600 na da nufin ƙara tsaro a makarantun gwamnati, domin kare dalibai, malamai da kayayyakin makarantu.
Gwamna Yusuf ya ja hankalin sabbin ma’aikatan da su nuna ƙwarewa da jajircewa, yana mai cewa aikin su zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta ilimin Kano.
Ya ƙara tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da saka hannun jari a gine-ginen makarantu, horar da malamai, da kuma ingantaccen tsarin kulawa da aiki, domin dawo da martabar ilimi a Kano.
Sanusi Bature Dawakin Tofa
Darakta-Janar na Yaɗa Labarai,
Gidan Gwamnatin Kano.




