Gwamna Yusuf: Mun Cika Sama da Kashi 80% na Alkawuran da mukayiwa kanawa a Ƙasa da Shekaru Uku

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta aiwatar da fiye da kashi 80% na alkawuran da ta yi wa al’umma a cikin kusan shekaru biyu da rabi kacal da hawa mulki.
Ya bayyana haka ne lokacin da ya gabatar da kasafin kuɗi na 2026 da ya kai ₦1.36 tiriliyan a gaban Majalisar Dokokin Kano.
A cewar mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, Gwamnan ya ce wannan cigaba hujja ce ta jajircewar gwamnatin jihar wajen inganta rayuwar jama’a.
Gwamna Yusuf ya bayyana kasafin kuɗin a matsayin alkawari da tsari na kammala muhimman ayyuka da gina tsarin da zai amfanar da jiha nan gaba.
Kasafin ya ware ₦934.6bn ga ayyukan ci gaba (capital) da ₦433.4bn ga kuɗin gudanarwa (recurrent).
Sashen ilimi ya samu kaso mafi yawa—₦405.3bn, wanda ya yi daidai da kashi 30% na gaba ɗaya kasafin.
Ya kuma gode wa ‘yan majalisa kan goyon bayan da suka bayar wajen aiwatar da kasafin 2025.




