Gwamnatin Kano Ta Ware Naira Biliyan 5.397 Don Gyaran Makarantu a Fadin Jihar

Majalisar zartarwa ta Jihar Kano ta amince da kashe jimillar kudin da ya kai Naira biliyan 5.397 domin gyaran manyan makarantun gwamnati a fadin jihar, ciki har da Government Day Science College.
Wannan mataki ya biyo bayan wani bidiyo da sanannen mai tasiri a kafafen sada zumunta, Bello Habib Galadanci (Dan Bello), ya wallafa watanni kadan da suka gabata, inda ya nuna mummunan yanayin da makarantar kimiyya ta gwamnati ke ciki.
Bayan fitowar bidiyon, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar gaggawa zuwa makarantar tare da Government Technical College (GTC), inda ya bayar da umarnin a fara gyaran makarantun nan take.
A yayin zaman majalisar zartarwa ta 32 da aka gudanar a ranar 4 ga Oktoba, 2025, gwamnati ta amince da kashe Naira miliyan 905 domin cikakken gyaran Government Day Science College, makarantar da aka kafa tun a shekarar 1993 a lokacin mulkin soja.
Sauran makarantun da suka amfana da wannan kudin sun haɗa da:
GSS Rimi, Sumaila – Naira miliyan 397 don gyaran gine-gine.
Government Technical College, Kofar Nassarawa (GTC Kano) – Naira biliyan 1.4 don gyaran makarantar.
Kwalejin noma ta Audu Bako, Dambatta – Naira miliyan 546 don sabunta ginin da kayan aiki.
Makarantun firamare a fadin kananan hukumomi 44 – Naira biliyan 1.8 karkashin shirin CRC, domin gyaran ajujuwa da samar da kayan aiki.
School for Arabic Studies (SAS), Birnin Kano – Naira miliyan 349 don gyaran gine-gine.
Gwamnatin jihar ta ce wannan shiri yana daga cikin manufofinta na inganta harkar ilimi da samar da yanayi mai kyau ga ɗalibai da malamai a Kano.