Hukumar tsaron farin kaya ta ƙasa reshen Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar jami’inta wanda wasu Yan ta’adda suka yi wa kisan gilla a jahar.

Hukumar tsaron farin kaya reshen Jihar Jigawa ta bayyana tsananin bakin cikinta na asarar rashi da hukumar tayi game da kisan gilla da akayiwa jami’inta SC Bashir Adamu Jibril Wanda Ke aiki Sashin bincike na hukumar.
A ranar Litinin, 4 ga watan Agusta, 2025, da misalin karfe 13:00, SC Bashir Adamu Jibril yana gudanar da aikinsa a kusa da Kasuwar Shuwarin da ke karamar hukumar Kiyawa, inda wasu ’yan daba suka kai masa hari.
Harin dai ya biyo bayan nasarar cafke wani da ake zargi da aikata laifi, lamarin da ya janyo tayar da jijiyar wuya a tsakanin gungun ‘yan ta’addan wadanda suka saɓa wa bin doka da oda tare da nufin hana wanzuwar adalci.
‘Yan ta’addan dauke da sanduna da sauran muggan makamai da aka kirkira a cikin gida, sun farwa kan jami’in, inda suka yi masa mummunar illa da ta kai ga mutuwarsa nan take.
Nan take aka kai shi babban asibitin Dutse, inda jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwarsa.
Bayan daukar matakin gaggawa da tattara bayanan sirri, tun daga lokacin da jami’an tsaro suka kama babban ƴan-taaddan wanda ake zargi kuma wanda ya shirya harin.
Ana ci gaba da gudanar da bincike, domin tabbatar da kamo sauran wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Hukumar tsaron farin kayan ta yi matukar takaicin wannan rashi mai raɗaɗi kuma tana yin Allah wadai da wannan kisan gillan da aka yi wa wannan jami’i nata wanda yake bakin aiki.
Hukumar tana tabbatar wa jama’a da iyalan mamacin cewa za ta tsaya tsayin daka har sai ta tabbatar da an yi adalci, kuma ba za a yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an gurfanar da duk masu hannu a cikin wannan danyen aikin.
Marigayi SC Bashir Adamu Jibril ya shahara da jajircewa, da’a, da jajircewa wajen yiwa kasa hidima.
Rashin nasa ba wai kawai Jami’an tsaro ne suka yi rashin ba, wannan rashin abin takaici ne ga kowa da kowa musamman a Jihar Jigawa.
Allah Ta’ala Ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma sa ya huta, Allah yasa Aljannatul Firdausi ta zama masaukin shi.
A cewar jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ASC Badrudddeen Tijjani Mahmud.




