Ketare

Trump ya ce dangantakarsa da Musk ta kare

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce dangantakarsa da Elon Musk ta kare.

Sharhin sun kasance na baya-bayan nan daga Trump tun bayan rikicin da ya barke tsakanin sa da Musk a kafafen sada zumunta.

Hakan Ya zo ne bayan da attajirin wanda ya ba da gudummawar miliyoyin daloli ga yakin neman zaben Trump kuma ya zama mataimaki a Fadar White House – ya soki kudirin haraji da kashe kudi na shugaban kasa a fili, wata muhimmiyar manufar cikin gida.

Yawancin ‘yan jam’iyyar Republican sun bi bayan shugaban kasar saidai Mataimakin Shugaban Kasa JD Vance ya ce Musk ya “yi kalamai masu tsauri sosai” kuma watakila Hakan ba zai sa a sake maraba da shi ba.

A ranar Alhamis, duk da haka, Trump ya shaida wa ‘yan jarida cewa yana “baƙin ciki” da halayyar Musk.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button