Labarai

Gwamnatin jihar Benue ta ce har yanzu mutane 107 da aka jikkata a hare-haren da aka kai garin Yelwata, na samun kulawa a asibitin koyarwa na jihar da ke Makurdi.

Babban sakataren ma’aikatar jin-ƙai da kare afkuwar bala’i, Mista James Iorpuu ne ya bayyana haka yayin tattaunawa da manema labarai a Makurdi, babban birnin jihar.

Wasu da ake zargin ƴanbindiga ne sun afka wa jihar ranar 13 ga watan Yuni, inda suka kashe mutane sama da 100 a garin Yelwata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Iorpuu ya ce jihar ta fara fuskantar hare-hare daga ƴanbindiga tun shekarar 2011.

Ya yi fatan kada a sake samun irin abin da ya faru a Yelwata, wanda ya ce ba a taɓa ganin irinsa ba a duniya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button