Labarai
Jami’ai a kasar Malawi sun ce ƙasar ta samu nasarar cimma abin da Majalisar Dinkin Duniya ta gindaya wajen yaƙi da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDS.

A baya ƙasar ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da cutar HIV ta fi muni, inda mutum guda cikin bakwai na ƴan ƙasar ke ɗauke da cutar a shekarun 1990.
Lamarin da ya sa tsawon shekarun ƴan ƙasar ya ragu daga 56 zuwa 38 a shekarun na 1990.
Shugabar hukumar yaƙi da cutar a ƙasar, Beatrice Matanje ta ce ƙasar ta yi ƙoƙari wajen dagewa kan matakan rage yawan masu ɗauke da cutar.
Cikin ƙa’idojin yaƙi da cutar da Majalisar Dinkin Duniya ta gindaya, kuma ƙasar ke son cimmawa a wannan shekara har da tabbatar da aƙalla kashi 95 cikin ɗari na masu ɗauke da cutar su san matsayinsu.
Ms Matanje ta kuma ce akwai buƙatar ɗaukar matakai kan ƴan mata da sauran mata domin kare su daga kamuwa da cutar.




