Ketare

Ayyukan Rasha na yaƙi a Ukraine ‘abin kyama ne’, in ji Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar sabbin takunkumi yayin da yake sukar ayyukan sojan Rasha a Ukraine a matsayin “abin kyama”.

“Rasha – Ina ganin abin da suke yi abin kyama ne. Ina ganin abin kyama ne,” Trump ya shaida wa ‘yan jarida a ranar Alhamis, ranar da hare-haren Moscow a kan Kyiv suka kashe fiye da mutane goma sha biyu.

Trump ya kuma ce zai tura jakadansa na musamman, Steve Witkoff, wanda yake a Isra’ila a halin yanzu, don ziyartar Rasha a gaba.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya riga ya gana da Witkoff sau da dama a Moscow, kafin kokarin Trump na gyara dangantaka da Kremlin ya tsaya cik.

Washington ta ba Moscow wa’adin zuwa ƙarshen mako mai zuwa don dakatar da hare-hare a Ukraine, tare da barazanar sanya takunkumin tattalin arziki mai tsanani.

Trump ya maimaita wa’adin a ranar Alhamis.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button