Labarai
Farashin danyen mai ya fadi a kasuwar duniya yau Litinin, sakamakon tsammanin karin yawan fitar da danyen mai daga kungiyar OPEC a watan Agusta, duk da rashin tabbas kan bukatar.

Farashin ganga ya sauka da senti 13 ko kashi 0.19%, inda ya tsaya akan dala $66.67.
A makon da ya gabata, dukkan wadannan farashin sun fuskanci mafi girman faduwa cikin mako guda tun watan Maris 2023.
Wani rahoto daga Reuters ya bayyana cewa wakilai hudu daga kungiyar OPEC+ sun ce kungiyar na shirin kara fitar da ganga 411,000 a kowace rana a watan Agusta, kamar yadda ta yi a watannin Mayu, Yuni da Yuli.
OPEC+ na shirin ganawa a ranar 6 ga Yuli, wanda zai zama karo na biyar da kungiyar ke kara yawan fitar da mai tun bayan da suka fara sassauta takunkumin rage fitar da mai a watan Afrilu.




