Labarai

Majalisar Dattawan ta yi Allh da wata zanga-zanga da aka yi a Ghana, inda wasu ke buƙatar a kori ’yan Nijeriya daga ƙasar.

Shugaban kwamitin majalisar kan ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje, Sanata Bassey Aniekan, ya ce ba daidai ba ne a zargi dukkan ’yan Nijeriya saboda laifin wasu ƙalilan.

Ya ce ’yan Nijeriya mutane ne masu zaman lafiya, masu aiki tuƙuru, kuma suna taka rawar gani a ƙasashen da suke ciki, ciki har da Ghana.

Sanatan ya buƙaci ’yan Ghana da su tuna alaƙa ta tarihi, tattalin arziƙi da al’adu da ke tsakanin Nijeriya da Ghana.

Ya kuma shawarci ’yan Nijeriya da ke Ghana da su kwantar da hankali, kada su ɗauki fansa, yana mai tabbatar musu cewa gwamnatin Nijeriya na tattaunawa da hukumomin Ghana domin magance matsalar cikin lumana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button