Isra’ila ta hallaka wasu Falasdinawa bakwai da yunwa a Gaza

Asibitocin Gaza sun bayyana sabbin alkalumma na mutuwar mutane bakwai “saboda yunwa da rashin abinci mai gina jiki”, wanda ya kai adadin mutuwar da ta shafi yunwa zuwa 154, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta yankin.
A halin yanzu, hare-haren Isra’ila na ci gaba inda akalla Falasdinawa 21, ciki har da fiye da goma sha biyu masu neman agaji, suka mutu tun daga wayewar gari a fadin Zirin Gaza, a cewar majiyoyin kiwon lafiya da suka yi magana da Al Jazeera.
Firaministan Biritaniya Keir Starmer ya shaida wa majalisar ministocinsa cewa Biritaniya za ta amince da ƙasar Falasdinu nan da watan Satumba sai dai idan Isra’ila ta dauki “matakan a-zo-a-gani” don kawo karshen yakin da take yi a Gaza kuma ta kuduri aniyar aiwatar da wani tsari na zaman lafiya mai dorewa.
Yakin Isra’ila a Gaza ya kashe akalla mutane 60,034 kuma ya jikkata wasu 145,870. An kiyasta cewa mutane 1,139 ne aka kashe a Isra’ila yayin harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoba, 2023, kuma fiye da 200 aka kama su.




