Labarai

Gwamnatin Taraya ta bayyana cewa lokaci ya yi da ‘yan bindiga da ke addabar Arewacin kasarnan zasu daina kashe mutane su kuma miƙa wuya.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ne ya faɗa hakan a hirarsa da BBC Hausa, inda ya ce gwamnatin ta samu nasarar rage hare-haren ta’addanci da na ‘yan bindiga.

Ya ce a da ana kai hari a gidajen yari da jirgin ƙasa da sansanonin sojoji, amma yanzu an daƙile hakan tun bayan da wannan gwamnati ta hau mulki.

Ya ƙara da cewa gwamnati ta kashe shugabannin ‘yan bindiga kimanin 300.

Har ila yau, Ribadu ya ce yanzu mutane suna iya zuwa gonakinsu a wuraren da a baya ba a iya shiga saboda barazanar ‘yan bindiga.

Sai dai duk da wannan ikirari, har yanzu wasu yankunan kamar Zamfara, Benuwe da Filato na fama da hare-haren ‘an bindiga da rikicin ƙabilanci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button