Liverpool ta amince da ɗaukar Wirtz kan fam miliyan 116

Zakarun Gasar Premier, Liverpool sun amince su ɗauki ɗan wasan Jamus, Florian Wirtz kan fam miliyan 116 daga Bayer Leverkusen.
Da fari kudin ya ƙunshi fam miliyan 100 na sayen ɗan wasan, sai kuma ƙarin fam miliyan 16 idan ƙungiyar na samu cimma wasu nasarori.
Idan har Liverpool ta biya duka, kuɗin ɗan wasan zai kasance mafi tsada aka saya a tarihi a Birtaniya.
Yanzu haka ɗan wasan da ya fi tsada a kuɗin sayensa na farko shi ne Enzo Fernandez, ɗan Argentina da Chelsea ta saya daga Benfica a 2023.
Daga nan sai Moises Caicedo shi ma da Chelsea ta saya daga Brighton kan fam miliyan 100 da farko, wanda ake ganin kuɗinsa zai iya ƙaruwa zuwa fam miliyan 115.
Cinikin zai kasance mafi tsada da Liverpool ta saya a tarihi.
A yanzu Darwin Nunez da ta saye daga Benfica kan fam miliyan 64 daga baya ya kai fam miliyan 85 ne ɗan wasa mafi tsada da ƙungiyar ta saya, sai kuma Virgil van Dijk da ta saya daga Southampton 2018.
Kamar yadda labarin ya zo a rahoton BBC Hausa (https://www.bbc.com/hausa/live/clygj3rv3n4t?at_campaign=ws_whatsapp)