Labarai

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan ya bayyana kashe sama da mutune 30 da ƴanbindiga suka yi daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da su a matsayin rashin sanin darajar ɗan’adam.

Gwamna Dauda ya bayyana haka ne bayan wasu ƴanbindiga a jihar sun kashe wasu mutane da ke hannunsu, lamarin da gwamnan ya ɗauki alwashin cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai makasan sun ɗanɗana kuɗarsu.

An yi garkuwa da gomman mutanen ne a ƙauyen Banga kimanin watanni huɗu da suka gabata, kafin ƴanbindigar suka kashe su saboda ba a biya kuɗin fansa ba.

Rahotanni sun ce da yawa daga cikin mamatan yankar rago aka yi musu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button