Dakarun Sojin Saman kasarnan sun ce sun ƙaddamar da gagarumin farmakin sama kan sansanonin ‘yan bindiga a jihar Neja a ranakun Laraba da Alhamis, a wani yunƙuri na kawar da ƴan fashin da suka kai hari kan dakarun ƙasar a baya-bayan nan.

A wata sanarwa da rundunar sojin saman ta wallafa a shafinta na sada zumunta ta ce an kai harin ne ƙarƙashin shirin FANSAN YAMMA “domin kawar da barazanar tsaro da ‘yan ta’adda ke haifarwa.
A cikin makon nan ne aka samu rahotannin da suka ce ƴan fashin daji a jihar ta Neja, arewa maso tsakiyar Najeriya sun kai samame a wasu sansanonin sojin Najeriya inda suka kashe jami’an soji “aƙalla 17”.
Wata sanarwa da rundunar sojin ƙasa ta Najeriyar ta fitar ta tabbatar da kai harin sai dai ba ta yi bayani kan yawan sojojin da suka rasa rayukansu ba sanadiyyar farmakin.
Neja na cikin jihohin Najeriya masu fama da matsalar tsaro, inda ƴan bindiga suka tarwatsa ƙauyuka da dama, lamarin da ya haifar da asarar ɗimbin rayuka da kawo cikas ga ayyukan tattalin arziƙi.




