Labarai

An gano gwawar mutum 15 a yayin da ake ci gaba neman wasu uku bayan hastarin kwalekwale da ya auku a yankin Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja.

Kwalekwalen ya kife ne a yayin da yake ɗauke da mutune 43 da buhuna 60 na shinkafa da shanu uku da tumaki biyu a ranar Asabar.

Kifewar kwalekwalen ta auku ne a sakamakon karonsa da wani kututture bayan ya ɗauki fasinjojin daga yankin Guni zai kai su kasuwar mako-mako da ke yankin Zumba da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro.

Manajan Hukumar Albarkatun Koguna ta Ƙasa (NIWA), mai kula da yankin, Akapo Adeboye, ya ce an gano gawarwakin mutane 15, amma ana ci gaba neman wasu mutane uku, ko da yake cewa an yi nasarar ceto mutane 26 da ke sanye da rigunan kariya da ransu, bayan aukuwar hatsarin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button