Labarai
An fara zaman jin ra’ayoyi na kwanaki biyu a nan Kano domin sake duba Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, da nufin daidaita shi da bukatun zamani.

Wannan taro na yankin Arewa maso Yamma da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sauya Kundin Tsarin Mulki ya shirya karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa sanata Barau Jibrin yana gudana ne a dakin taro na Bristol Palace Hotel da ke cikin birnin Kano.
Taron ya samu halartar wakilai daga jihohi bakwai na yankin: Kano, Jigawa, Kaduna, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara, ciki har da kungiyoyin fararen hula, masu ruwa da tsaki, sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin ƙwararru, waɗanda ke tattaunawa kan shawarwarin da suka gabatar domin sauya wasu muhimman sassa na kundin tsarin mulki.




