Ketare

Wane adadin Uranium ake buƙata kafin mallakar nukiliya, nawa Iran ke da shi?

A ranar Juma’a 13 ga watan Yuni ne, Isra’ila ta bayyana cewa ta ƙaddamar da hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran da na sojin ƙasar, da nufin ruguza shirin nukiliyarta da ƙarfin sojinta, lamarin da ya haifar da musayar wuta tsakanin ƙasashen biyu.

Hare-haren na zuwa ne bayan da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya, (IAEA) ta amince da ɗaukar mataki kan Iran saboda “rashin biyayya” ga abin da aka wajabta mata ƙarƙashin wani shirin haɗin gwiwa na (JCPOA), ciki har da zarta kashi 3.67 na abin da aka ƙayyade mata na sarrafa sinadarin Uranium.

Batun inganta sinadarin uranium ya kasance gaɓar da aka fi samun saɓani tsakanin Amurka da Iran a lokacin tattaunawar nukiliyarta, wani saɓani da har yanzu ba a samu daidaito ba, duk kuwa da zama har sau biyar da aka yi kan batun.

Taƙaita yawan sinadarin ya kasance babban abin da aka fi samun saɓani a tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran na tsawon shekara 20.

Me muka sani kan yawan adadin sinadarin uranium na Iran? Me ya saya batun ya zama gaɓar da aka fi samun saɓani? Kuma me ya sa ƙara adadin uranium din Iran zuwa 60 ya zama abin damuwa ga Amurka, Isra’ila da hukumar IAEA?

Mene ne makamashin uranium, kuma daga ina ake samun sa?

Uranium wani ma’adini ne mai ƙunshe da wasu ƙwayoyin sinadarai da Allah ya halitta ake kuma samun sa a cikin duwatsu da ƙasa da ma cikin teku.

Duk da yawan da ma’adinin da ake da su a duniya, ana tono shi ne kawai a wasu taƙaitattaun yankuna.

Yankunan da aka fi samun ma’adinin sun haɗa da Kazakhtans da Canada da Australia da wasu ƙasashen Afirka masu yawa. Ita ma Iran na da yankuna masu ɗauke da sinadarin, kuma tana tono shi.

Ma’adinin uranium a ainihin yadda yake ba zai iya samar da makamashi ko makami ba har sai an sarrafa shi, saboda fiye da kashi 99 na ƙananan sinadaran da ke cikinsa, babu makamashi jikinsu, wato uranium-238.

Abu mai muhimmanci a cikinsa shi ne sinadaran uranium-235, wanda kuma su ne sinadarai marasa yawa a jikin kowane uranium, wanda bai fi kashi 0.7 ba, kuma zai iya samar da makamashi.

Idan aka tattara sinadaran uranium-235 suka kai wani mataki, za su iya samar da makamashi mai yawa.

Ana amfani da wannan makamashin domin samar da wutar lantarki, amma game da makamin nukiliya, sinadarin ake yi wa wasu haɗe-haɗe ta yadda za su samar da mummanar fashewar da za ta haifar da gagarumar ɓarna.

Mene ne yawansa, kuma wane mataki ne ba a so ya zarta?

Ko ma wane amfani za a yi da shi, dole ne a sarrafa uranium domin ƙara adadin ƙwayoyin uranium-235, wani mataki da aka fi sani da yawaita sinadarin.

Akan ƙara yawan sinadarin ta hanyar amfani da iskar gas wanda ke jujjuyawa cikin sauri, yana rarraba tare da ware ma’adinin sinadarin uranium-235 da kuma uranium-238.

Akan karkasa matakan ƙaruwar uranium kamar haka:

Uranium na ainihi: Yana ɗauke da kashi 0.7 cikin 100 na ƙananan sinadaran (uranium-235), kuma a wannan mataki ba a amfani da shi wajen makamashi ko makamai.

Adadi kaɗan (har zuwa kashi 5 cikin 100): Akan yi amfani da wannan mataki ga tashoshin samar da lantarki. Kashi 3.67 ne adadi mafi yawa da aka yarje wa Iran ƙarƙashin yarjejeniyar 2015.

Matsakaicin adadi (zuwa kashi 20 cikin 100): Masu bincike kan yin amfani da wannan adadi wajen samar da sinadaran haɗa wasu magunguna da wasu manhajojin kamfanoni, hanya ce ta kai wa matakin mafi yawa.

Babban mataki (sama da kashi 60 cikin 100): Wannan ya yi kusa adadin da ake buƙata domin samar da makamin nukiliya. A baya-bayan nan an bayyana cewa Iran ta kai wannan adadi, inda hakan ya haifar da damuwa ga ƙasashen yamma da hukumar IAEA, wanda suke ganin tamkar ƙasar ta kama hanyar mallakar makamin nukiliya ne.

Ƙololuwar mataki (zuwa kashi 90 cikin 100): Wannan mataki ne da ake amfani da shi wajen ƙera makamin nukiliya. Hukumar IAEA na ganin mallakar kilogiram 25 na sarrafaffen sinadarin zai wadatar wajen ƙera makamanin nukiliya. Yawan sinadarin uranium ɗinka, ƙaruwar samun sauƙin ƙera makamin nukiliyarka.

Me ya sa kashi 60 da Iran ta mallaka ya zama a bin damuwa?

Adadin sarrafaffen uranium da ake buƙata domin ƙera makamin nukiliya shi ne sinadarin uranium-235 ya kai kashi 90 cikin 100.

Akan yi amfani da wannan adadi a kamfanin ƙera makamin nukiliya, saboda idan ya kai wannan mataki zai zama mai hatsari, ta yadda idan aka samu saɓani zai iya kai wa ga haifar da mummunar fashewa.

Kai wa wannan ba abu ne da za a iya cimma a lokaci guda ba, sai ta hanyar bin matakai daki-daki.

To amma a iya cewa adadin yawan sarrafaffun sinadaranka, shi ne zai sauƙaƙa maka da hanzarta zuwanka mataki na gaba.

Wannan shi ya sa mallakar kashi 60 cikin 100 da Iran ta yi ya zama abin damuwa, ba wai saboda kusantar mallakar makamin kawai ba, har ma da zarta adadin da ake buƙata na zaman lafiya.

Babu wata tashar samar da lantarki ko wani gagarumin aikin kamfani da ke buƙatar wannan adadi da ta mallaka.

Don haka kai wa wannan mataki ya haifar da ayar tambayar game da gaskiyar dalilinta na sarrafa sinadarin.

Ɗaya daga cikin damuwar ita ce, adadin da take da shi na kashi 60 zai rage adadin lokacin da za ta iya ɗauka wajen ƙera makamin, zuwa makonni ƙalilan, idan har ta ƙudiri aniyar yin hakan.

Ita dai Tehran ta dage cewa shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne.

Me IAEA ta ce kan matakin da Iran ta kai a mallakar makamashin?

A ranar Larabar nan ne shugaban hukumar sa ido kan makamin nukiliya ta duniya, IAEA, Rafael Grossi ya ce babu shaidar da ke nuna ƙasar Iran tana da makamin nukiliya ko kuma tana dab da mallakar sa.

To sai dai kuma hukumar ya IAEA cikin rahotonta na watan Mayun 2025, ta ce Iran ta tara sinadarin sarrafaffen uraniun da ba ta taɓa samun adadinsa ba a tarihi.

A cewar rahoton hukumar adadin sinadarin da ƙasar ta mallaka ya kai kilogiram 9,247.6, zuwa ranar 17 ga watan Mayu, ƙari a kan kilogiram 953.2 da take da shi a shekarar da ta gabata.

Abin da ya fi damun ƙasashen yamma da hukumar IAEA shi ne mallakar kashi 60 da Iran ta yi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button