Labarai

Rundunar yan sanda ta kasa reshen Jihar Jigawa ta kama wani mutum mai suna Iliyasu Musa, ɗan shekara 40, bisa zargin kashe matarsa Hadiza Sale, ƴar shekara 30, a ƙauyen Afasha da ke ƙaramar hukumar Aujara.

Wanda ake zargin ya shafe sama da makonni biyu yana ɓuya tun bayan da lamarin ya faru a ranar 10 ga Yuli, 2025.

Ana zargin mutumin da kashe matarsa da sanda a daren ranar da ta dawo daga kasuwa, lamarin da ya girgiza al’ummar yankin.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar na jahar Shisu Lawan Adam ya fitar ta bayyana cewa jami’an ‘yan sanda daga ofishin Aujara ne suka samu nasarar kama shi a ranar Talata, 23 ga Yuli, 2025 a ƙauyen Larabar-Tambarin-Gwani.

Rundunar ta kuma tabbatar da cewa Iliyasu yana hannunsu a sashen Binciken laifuka na Jiha da ke Dutse, inda ake ci gaba da gudanar da bincike kafin a gurfanar da shi gaban kotu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button