Hukumar Shari’a ta jihar Kano tayi zama da Shugabannin makarantun Islamiyyu na jihar Kano domin gyara al’amuran saukar Alƙur’ani da makarantun ke yi, musamman wajen tsauwalawa Iyayen yara hidimar da tafi karfinsu, da kuma shigar da wadanda ba su cancanci saukar ba cikinta.

Zaman ya gudana ne a ofishin hukumar dake nan Kano, inda Shugaban Hukumar Sheikh Abbas Abubakar Daneji yace akwai bukatar a kawo gyare gyare domin duba Al’amuran.
Ya ce hukumar ba za ta ci gaba da zuba ido ana cakuɗa maza da mata a wurin da ake gudanar da saukar ba, da daukar hotuna barkatai musamman ta haɗa jiki a tsakanin maza da mata.
Daga bisani hukumar tayi wani tsari na bayar da shaidar sahalewar yin bikin saukar Alƙur’ani bayan tabbatar da bin tsari daga hukumar shari’a.