Labarai

Allah yayiwa sarkin Gusau Alhaji Ibrahim Bello rasuwa Mai shekaru 71 da haihuwa

Gwamnatin jahar Zamfara ta tabbatar da rasuwa sarkin Gusau Alhaji Ibrahim Bello Mai shekaru 71 da haihuwa ya rasu sakamakon rashin lafiya a wani asibiti dake babban birnin tarayya Abuja.

An haifi marigayin Alhaji Ibrahim Bello a shekarar 1954, sannan an nada shi a matsayin Sarkin Gusau na 15 a ranar 16 ga Maris, 2015, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya naɗashi.

An naɗa Shi matsayin Sarkin ne bayan rasuwar dan’uwansa, Alhaji Muhammad Kabiru Danbaba, wanda ya rasu a Abuja a ranar 5 ga Maris, 2015.

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a cikin wani rubutu a shafukan sa na sada zumunta da aka tabbatar, ya bayyana ta’aziyya kan rasuwar sarkin gargajiya, ya bayyana cewa “Hakika, mu daga Allah muke kuma gareshi za mu koma.”

“Allah ya jiƙan Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau, Dr. Ibrahim Bello. Allah ya gafarta masa, ya ba shi wurin hutawa mai kyau, ya kuma shigar da shi Aljannatul Firdaus. Ameen,” gwamnan ya rubuta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button