Labarai
Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jama’atul Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah Sheik Sani Yahaya Jingir, ya ce ba zai goyi bayan takarar Bola Tinubu ba a zaben 2027 matukar ya canza Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taron wa’azi a masallacinsa na ’Yan Taya da ke Jos, babban birnin jihar Filato.
Idan zaa iya tunawa a zaben 2023 da ya gabata Sheikh Jingir ya goyi bayan Tinubu sannan ya umarci magoya bayansa da su ma su yi haka a wancan lokacin.
Jita-jitar da ake yadawa dai a kan cewa akwai yiwuwar Tinubu ya ajiye Kashim din a matsayin abokin takararsa a zabe mai zuwa ta dada kamari a ’yan kwanakin nan.


