Labarai

Jam’iyyar APC ta naɗa Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa, bayan taron da aka gudanar a Abuja tare da shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jam’iyyar.

Yilwatda, wanda ya fito daga jihar Filato, ya maye gurbin Dr. Abdullahi Umar Ganduje wanda ya yi murabus a watan Yuni 2025 saboda dalilan lafiya. Kafin naɗinsa, Yilwatda na rike da mukamin Ministan Jin ƙai da Rage Talauci a gwamnatin Tinubu.

Farfesa Nentawe ya kasance ɗan takarar gwamna a jihar Filato a zaɓen 2023 karkashin APC. Hakanan, ya taba zama kwamishinan zaɓe na hukumar INEC daga 2017 zuwa 2021, inda ya jagoranci harkokin zaɓe a jihohi da dama.

Naɗin nasa ya zo ne da nufin ƙarfafa haɗin kai da daidaiton wakilci a jam’iyyar, kasancewar yankin Arewa ta Tsakiya ke da hakkinta a kujerar shugaban jam’iyya.

Hakanan kasancewarsa Kirista na ba da gudunmawa wajen daidaita wakilcin addinai a cikin jam’iyyar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button