Labarai
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa kawo ƙarshen ta’addanci da hare-haren ‘yan bindiga yana daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali a kai.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin ƙaddamar da sabbin gidajen zama ga mutanen da hare-haren ‘yan bindiga ya shafa a Jihar Kaduna.
Tinubu, wanda mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya wakilta, ya ce: “Yaƙi da ta’addanci babban ƙalubale ne, amma kawo ƙarshensa babban abu ne a cikin ajandar tsaron ƙasa.
Wannan aikin gine-ginen an yi shi ne tare da haɗin gwiwar Qatar Charity Organisation, a matsayin wani ɓangare na shirin gwamnatin tarayya na farfaɗo da al’ummar da rikice-rikice suka shafa.
Tinubu ya ce an samu ci gaba sosai wajen dawo da zaman lafiya da taimaka wa mutane su farfaɗo da rayuwarsu a Jihar Kaduna.




