Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Usman Alhaji, ya yi watsi da cire shi daga matsayin Wazirin Gaya,
Har yanzu nine wazirin masarautar gaya

Tsohon sakataren gwamntin jihar kano Usiman alhaji
Alhaji yana mai cewa wannan mataki ba shi da wani tasiri kuma aikin banza ne.
Martaninsa ya biyo bayan sanarwar da Majalisar masarautar Gaya tare da goyon bayan Gwamnatin Jihar Kano suka fitar kwanan nan, inda suka bayyana cire masa sarautar gargajiya.
Wannan mataki ya biyo bayan sukar da Usman Alhaji ya yi wa Gwamnatin Jihar Kano a bainar jama’a dangane da abin da ya bayyana a matsayin “barnar” wani bashin wajen dala miliyan 600 da ake zargin an karɓa ba tare da bin ka’ida ba.
A cikin wata sanarwa da Ibrahim Dan’azumi Gwarzo ya fitar a madadin kungiyar ta APC Patriotic Volunteers — ƙungiyar da Usman Alhaji ya kafa — tsohon SSG ɗin ya bayyana cewa matakin ya samo asali ne daga siyasa kuma babu wata doka da ke goyon bayansa
Sanarwar ta kara da cewa cire shi daga sarauta an yi ne ba tare da bin ƙa’idoji ba kuma an yi hakan ta hanyar da ta nuna bambanci da rashin adalci.
Kungiyar ta danganta batun da dokar da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta zartar, wadda ta soke ƙarin masarautu huɗu — Gaya, Rano, Karaye da Bichi — tare da mayar da su daga masarautun aji na farko zuwa na biyu, a matsayin tushen matsalar.




