Iran ta shirya yaki da Isra’ila, ba za ta dakatar da shirin nukiliyarta ba: Pezeshkian

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce kasarsa ta shirya don kowanne irin yaki da Isra’ila za ta iya kaddamar da shi a kanta, yana mai cewa ba shi da fata kan tsagaita wutar da ke tsakanin kasashen, yayin da ya tabbatar da cewa Tehran ta himmatu wajen ci gaba da shirin nukiliyarta don dalilai na zaman lafiya.
Pezeshkian ya yi wadannan maganganu a wata hira ta musamman da Al Jazeera ta watsa a ranar Laraba, wanda shine hira ta farko da shugaban Iran ya yi a talabijin tun bayan karshen rikicin kwanaki 12 da Isra’ila a watan da ya gabata, inda Amurka ta shiga tsakani a madadin Isra’ila, ta kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran.
Wadannan maganganun sun zo ne yayin da kasashen yammacin duniya ke cewa suna neman mafita ga burin nukiliyar Iran da ke ci gaba bayan rikicin, a yayin da ake samun rahotanni cewa hare-haren da aka kai kan cibiyoyin nukiliyarta ba su yi mummunar illa kamar yadda Washington ta yi ikirari ba.
Ya kara da cewa hare-haren Isra’ila, wadanda suka kashe manyan shugabannin soja da masana kimiyyar nukiliya, kuma suka lalata wuraren nukiliya, sun yi kokarin “kawar da” tsarin mulkin Iran, “amma sun kasa yin hakan kwata-kwata”.



