Labarai
Yar majalisar Dattawan Najeriya Sanata Natasha Akpoti ta ci alwashin komawa majalisar ranar Talata mai zuwa duk da dakatarwar da aka yi mata.

Sanatar mai wakiltar mazaɓar jihar Kogi ta tsakiya ta ce za ta yi hakan bisa hukuncin kotu, wadda ta ce dakatarwar wata shida da majalisar ta yi mata ta saɓa dokar tsarin mulkin Najeriya.
Sai dai majalisar ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin, wanda ya biyo bayan zarge-zargen cin zarafi da ta yi wa Shugaban Majalisa Godswill Akpabio da ɓata suna.
Da take magana da manema labarai a ranar Asabar, Natasha ta ce ba ta dakatar da aiki ba duk da ba ta zuwa zauren majalisar.



