Labarai

Gwamnatin Jihar Kano, ta sanar da cewa dukkanin makarantun firamare da sakandare, na gwamnati da masu zaman kansu, za su fara hutun ƙarshen zangon karatu na uku a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, 2025.

Wannan sanarwar ta fito ne daga Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru.

An buƙaci iyaye da ke da yara a makarantun kwana da su zo su ɗauki ‘ya’yansu da wuri a ranar da aka fara hutun.

An kuma umarci ɗaliban makarantun kwana da su dawo makaranta a ranar Lahadi, 7 ga watan Satumba, 2025, yayin da ɗaliban da ke zuwa daga gida za su koma a ranar Litinin, 8 ga watan Satumba, 2025.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button