Ketare

Ministan harkokin wajen Iran ya ce za a ci gaba da inganta makamashin nukiliya

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran ba za ta iya daina shirin ta na inganta sinadarin uranium ba, wanda hare-haren sama na Amurka da Isra’ila suka lalata sosai a watan da ya gabata.

“Yanzu an dakatar da shi saboda, lalacewar ta tsananta sosai, amma a bayyane yake, ba za mu iya daina aikinmu na ingantawa ba saboda nasara ce ta masana kimiyyar mu sannan kuma yanzu, fiye da haka, tambaya ce ta alfaharin kasa,” in ji Araghchi ga gidan talabijin na Amurka Fox News a wata hira da aka watsa a ranar Litinin.

Araghchi ya bayyana a hirar cewa Iran a “shirye take tayi magana” da Amurka, amma ba za su yi tattaunawa kai tsaye ba “a halin yanzu”.

“Muna a shirye mu dauki duk wani mataki na gina amincewa da ake bukata don tabbatar da cewa shirin nukiliyar Iran yana lafiya kuma zai kasance cikin zaman lafiya har abada, sannan Iran ba za ta taba neman makaman nukiliya ba, kuma a madadin haka, muna sa ran za su dage takunkumansu,” in ji ministan harkokin waje.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button