Sojojin Isra’ila sun kashe masu neman agaji 92 a Gaza yayin da mutane 19 suka mutu sakamakon yunwa

Rundunar Isra’ila sun kashe akalla Falasdinawa 115 a fadin Gaza, ciki har da mutane 92 da aka harbe su har lahira yayin da suke kokarin samun abinci a wurin ketarewa na Zikim a arewa da wuraren bayar da agaji a Rafah da Khan Younis a kudu.
Kashe-kashen da suka faru a ranar Lahadi sun zo ne yayin da ci gaba da kewayen Gaza da Isra’ila ke yi ya kara tsananta matsalar yunwa, inda hukumomin lafiya a can suka sanar da akalla mutuwar mutane 19 da yunwa a cikin kwanakin da suka gabata.
A Zikim, dakarun Isra’ila sun harbe akalla Falasdinawa 79, a cewar majiyoyin kiwon lafiya, yayin da jama’a suka taru a wurin da fatan samun fulawa daga wani ayarin agaji na Majalisar Dinkin Duniya.
An kashe wasu tara a kusa da wurin bayar da agajin a Rafah, inda wasu 36 suka rasa rayukansu awanni 24 da suka gabata. An kashe wasu hudu a kusa da wani wurin bayar da agaji na biyu a Khan Younis, a cewar Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Falasdinawa.



