Labarai

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce tarihin Najeriya ba zai cika ba da bai yi nasara a zaɓen 2023 ba.

Ya faɗi haka ne a ranar Lahadi a Ijebu Ode na Jihar Ogun, lokacin da ake gudanar da addu’o’in kwanaki takwas na rasuwar marigayi Sarkin Ijebu, Oba Sikiru Adetona.

Tinubu, ya yaba wa marigayin bisa goyon baya da albarkar da ya sanya masa kafin zaɓen 2023.

Tinubu, ya ce marigayin ya taka rawa sosai wajen ganin an samu dimokuraɗiyya a Najeriya, musamman a lokacin fafutukar ranar 12 ga watan Yuni.

Ya bayyana Sarkin a matsayin mai hikima, jajircewa da kuma shugabanci na gari.

Har ila yau, Tinubu ya godewa Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, bisa rawar da ya taka lokacin jana’izar Sarkin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button