Labarai
Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani da kaƙƙausar murya kan zargin da jam’iyyar haɗaka ta ADC ta yi mata akan rasuwar tsohon shugaban kasar wato Muhammadu Buhari.
Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani da kaƙƙausar murya kan zargin da jam’iyyar haɗaka ta ADC ta yi na cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu na amfani da rasuwar tsohon shugaba Muhammadu Buhari, don samun tagwamashi na siyasa da neman karɓuwa a idon jama'a.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya bayyana zargin ADC a matsayin “abun kunya,” inda ya ce jam’iyyar ce ke amfani da rasuwar Buhari don neman suna.
ADC dai ta ce gwamnatin Tinubu ta yi amfani da yadda aka gudanar da jana’izar Buhari da kuma yadda aka shirya bikin bankwana da shi a Daura da ke jihar Katsina, domin ƙara samun ƙarbuwa a idon ƴan ƙasa.
Fadar shugaban ƙasar ta ce marigayi Muhammadu Buhari ya cancanci yi masa jana’izar ban-girma kuma sun yi haka ne don girmamawa saboda hakan ne ya dace da shi a matsayinsa na tsohon shugaban ƙasa.




