Bangladesh: Mutane da dama sun mutu bayan jirgin sama ya faɗa kan wata makaranta

Akalla mutane 19 sun mutu kuma da dama sun jikkata a ranar Litinin lokacin da wani jirgin horo na rundunar sojin saman Bangladesh ya fadi a harabar wata makaranta a Dhaka, wanda ya zama hadarin jirgin sama mafi muni a kasar cikin shekaru da dama, in ji mahukunta.
Jirgin sama na F-7 BJI da aka kera a China ya tashi da karfe 1:06 na rana (0706 GMT) kuma ya fadi jim kadan a harabar Makarantar kwalejin Milestone School cibiyar ilimi ta cikin unguwar Uttara inda dalibai suke cikin aji a lokacin hatsarin Makarantar tana da dalibai daga firamare har zuwa aji na 12.
Bidiyon bayan hadarin ya nuna wata babbar wuta kusa da wani fili tana fitar da hayaki mai kauri zuwa sama, yayin da jama’a suka taru a gurin.
Za’a mika gawarwakin wadanda za a iya tabbatar da sunayensu ga iyalansu da wuri-wuri,” in ji shugaban rikon kwarya na Bangladesh Muhammad Yunus a kan X.
Sannan “Za a gano gawarwakin wadanda ba za a iya tantance su ba nan take ta hanyar gwajin DNA sannan kuma a mika su ga iyalansu.



