Labarai
Jami’an Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA ta yi nasarar kama wani sanannen dillalin ƙwayoyi ɗan shekaru 60, mai suna Okpara Paul Chigozie,

Jami’an rundunar musamman na hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) sun kama wani sanannen dillalin ƙwayoyi mai shekaru 60, mai suna Okpara Paul Chigozie, wanda ya kwashe shekaru bakwai yana guje wa hukuma,.
Sun kama shi ne lokacin da yake ƙoƙarin aika miyagun ƙwayoyi zuwa Kudu maso Gabas da wasu yankunan Nijeriya.
An kama Okpara ne a maboyarsa da ke lamba 72, titin Michael Ojo, Isheri, Ojo, Jihar Legas a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025.
NDLEA ta ce, binciken da aka yi da Karnukan gano ƙwayoyi ya gano kilo 7.6 na hodar iblis da gram 900 na methamphetamine a cikin ɓangarorin jikin motar da aka kama shi da ita.
Bayan haka, an kai samame a gidansa inda aka gano ƙarin kilo 1.8 na wata hodar iblis da kilo 1.3 na methamphetamine.




