Labarai
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya na samun cigaba sannu a hankali.

Ministan ya ya danganta hakan da sauye-sauyen da ake aiwatarwa a fannoni daban-daban ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, yayin da yake karɓar baƙuncin mambobi da sababbin shugabannin Ƙungiyar Editoci ta Nijeriya (NGE) da suka kai masa ziyarar a ofishin sa.
Yayin da ya amince cewa har yanzu akwai ƙalubale, Ministan ya ce gwamnati na samun cigaba a hankali kuma tana samun nasarar rage tsananin matsalolin da ake fuskanta.




