Ketare

Daliban Gaza sun fara rubuta jarabawa karo na farko tun bayan da yaƙi ya fara a watan Oktoba 2023

Daruruwan ɗaliban Falasɗinu a Gaza suna rubuta muhimmin jarrabawar ƙarshen makarantar sakandare da Ma’aikatar Ilimi ta yankin da aka kewaye ta shirya, da fatan shiga karatun jami’a.

A farkon wannan watan, ma’aikatar ta sanar da jarrabawar ranar Asabar, wadda za ta kasance ta farko tun bayan da Isra’ila ta fara yakin kisan kare dangi a Gaza bayan harin da Hamas ta jagoranta a kudancin Isra’ila a watan Oktoba na 2023.

Ma’aikatar ta tabbatar da cewa kimanin dalibai 1,500 ne suka yi rijista don rubuta jarrabawar, wadda za a gudanar ta hanyar lantarki ta amfani da kayan aikin kwamfuta na musamman, tare da ƙara da cewa an yi duk shirye-shiryen fasaha da suka wajaba don tabbatar da gudanarwa cikin sauƙi.

Wasu ɗalibai suna rubuta jarabawar kan layi a gida, yayin da wasu kuma suke rubuta ta a wurare daban-daban gwargwadon yankin da suke ciki, tare da la’akari da tsaro, duba da harin bama-baman da Isra’ila ke kaiwa kullum.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button